Matasan Kano ta Kudu sun goyi bayan komawar Kawu Sumaila jam’iyyar APC

0
75

Shugabannin matasa da magoya bayan Sanata Kawu Sumaila, dake Kano ta Kudu, sun tabbatar da cikakken goyon bayan su, ga ɗan majalisar tasu akan canjin shekar siyasar da yayi daga NNPP zuwa APC, inda suka ce wannan mataki da Sanata Kawu, ya dauka abu ne da zai kawo cigaban a’lummar yankin.

Matasan sun ce Sanatan yayi abun da ya dace wajen amincewa yayi tafiyar siyasa tare da shugaban ƙasa Tinubu, saboda cigaban da yake samarwa a’lumma.

Ɗaya daga cikin al’ummar Kano ta Kudu, da suka gudanar da gangamin zagayen nuna goyon baya ga Kawu Sumaila, Dr. Umar Ahmad Aliyu, wanda ɗaya ne daga cikin mutanen da gidauniyar Kawu Sumaila, ta ɗauki nauyin karatun su, ya bayyana cikakken goyon baya ga Sanatan nasu, yana mai cewa zasu yi biyayya ga duk matakin da ya yanke a siyasa.

Dr. Umar Ahmad Aliyu, ya ƙara da cewa komawar Kawu Sumaila cikin jam’iyyar APC, abu ne da zai inganta jam’iyyar a Kano ta Kudu, da jihar Kano baki ɗaya, saboda yana daga cikin mutanen da suka kafa jam’iyyar APC kafin ya shiga NNPP gabanin zaɓen shekarar 2023.

Matasan sun ce shugaban ƙasa Tinubu, ya samar da abubuwan alkairai a Kano ta Kudu, da yakai Naira biliyan 90 a ƙananun hukumomin Karaye da Rano, wanda hakan ke nuna cewa yankin ya samu abubuwan cigaba karkashin APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here