Kamfanin NNPCL zai fara haƙo man fetur a jihohin Arewa

0
72

Kimanin shekara biyu bayan ƙaddamar da aiki haƙo ɗanyen man fetur a kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba, sai dai a yanzu sabon shugaban kamfanin man na ƙasa Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin haƙo man a arewa.

Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin Najeriya sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasa ya dogara a kai.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.

Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ya sanar da cire tallafin man fetur.

A ranar Talata 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ce shugaban Najeriya na wancan lokacin, Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe wanda shi ne karon farko da aka fara aikin haƙar man a arewa.

Haka kuma bayan wannan, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa cikin a watan Maris na 2023 ne za a fara aikin haƙo ɗanyen man fetur a jihar Nassarawa da ke arewa ta tsakiya.

Sai dai tun daga lokacin, sai aka ji shiru, har aka yi zaɓe sabuwar gwamnati ta fara aiki, lamarin da ya wasu ƴan yankin suka fara tambayar ko dai dama an ɗanɗana musu zuma a baki ne kawai.

A game da wannan ne sabon shugaban kamfanin NNPCL, Injiniya Ojulari ya ce ƴan yankin su kwantar da hankalinsu domin za su koma bakin aikin kamar ya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here