Barazanar Turji ta sanya al’ummar Sokoto yin hijira

0
85

Tsoro da firgici ya shiga zuƙatan a’lummar wasu yankunan ƙaramar hukumar Isa dake jihar Sokoto, biyo bayan sabuwar barazanar da ƙasurgumin dan ta’adda Bello Turji, ya yi da hakan ya tilastawa mazauna yankin Bafarawa yin hijira daga gidajen su.

Mutanen sun shiga wannan yanayi na kunci a daidai lokacin da rundunar ƴan sandan Sokoto, tace ta aike da jami’an ta zuwa yankunan dake cikin matsalolin rashin zaman lafiya.

Wata majiya tace Bello Turji, ya umarci mazauna garuruwan Kamara, Arume, da  Kagara, su bar gidajensu kafin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ko su fuskanci tashin hankalin da basu zata ba.

Kakakin rundunar yan sandan Sokoto, ASP Ahmed Rufai, yace basu da masaniyar cewa Turji, yayi wannan barazana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here