Gobara ta tashi a barikin yan sanda na Ibadan

0
20

Wata gobara ta tashi da sanyin safiyar yau asabar, inda ta ƙone shaguna 6 a barikin yan sanda na Omolewa dake Ibadan.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ba’a samu asarar rayuka sakamakon gobarar ba.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka, ne ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin Ibadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here