Gwamna jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafin ɗaukar nauyin karatu a ƙasashen waje ga ɗalibai 9 da suka kammala karatun su da sakamako mafi daraja a jami’ar kimiyya da fasaha ta Ali Dangote da ke garin Wudil.
Gwamnan ya sanar da wannan tallafi ne yayin da ya ke jawabi a bikin yaye ɗaliban jami’ar karo na 5 da ke gudana a yau.
Daliban da suka samu nasarar tallafin karatun sun samu sakamako mafi daraja a fannonin karatu daban-daban.
Jami’ar ta kuma karrama Uban makarantar Aliko Dangote da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A yayin taron Ali Dangote, yayi alƙawarin tallafawa jama’ar da Naira biliyan 15 don samar mata da cigaba.