EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro

0
48
Ola Olukoyede

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta ɗauki alƙawarin yin bincike akan zargin da ake yiwa ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle, na cewa yana da hannu a wasu laifukan almundahanar kuɗaɗe, biyo bayan ƙorafi da kungiyar matasan jam’iyyar APC suka miƙawa hukumar suna neman a binciki Matawallen.Korafin da kungiyar APC-YLA, ta shigarwa EFCC ya zargi Matawalle da yin almubazzaranci da dukiyar talakawan jihar Zamfara da yawan su yakai Naira biliyan 528, a zamanin da yake gwamna.

EFCC ta bayar da tabbaci akan yin binciken bayan zanga-zangar da ya’yan kungiyar APC-YLA, suka gudanar a harabar shalkwatar hukumar yaƙi da cin hancin dake Abuja a ranar juma’a data gabata, karkashin jagorancin Mohammed Irelji.

A yayin zanga-zangar matasan sun roƙi hukumar EFCC da ta sake binciken zargin cin hanci da ake yiwa ƙaramin ministan tsaron.

Mai riƙon muƙamin daraktan tsaro na hukumar EFCC Idowu Adedeji, shine ya karbi korafin matasan, tare da yin alkawarin ɗaukar matakin daya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here