Nijar da Iran sun ƙulla yarjejeniya akan tsaro

0
53

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanya hannu akan wata yarjejeniyar ƙarfafa haɗin gwuiwa tsakaninta da kasar Iran wajen yaƙi da harkokin ta’addanci.

Yarjejeniyar ta kuma hadar da yaƙar miyagun ƙwayoyi da yanayin shige da fice ba bisa ka’ida ba.

A jiya ne ƙasashen biyu suka cimma wannan matsaya yayin wata ganawa tsakanin ministan harkokin cikin gida na Nijar da tawagar Iran a ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janarar Ahmad Reza Radan a birnin Yamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here