Gwamnatin Kano ta hana kafafen yaɗa watsa shirye-shiryen siyasa kai tsaye 

0
30
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano, ta sanar da dakatar da yaɗa shirye-shiryen siyasa kai tsaye, a kafafen yada labarai na jihar, inda tace anyi hakan don hana kawo ruɗani ga yaɗa shirye-shiryen da ka’iya haifar da hargitsi ga addini da al’ada.

Gwamnatin ta sanar da ɗaukar matakin yayin gabatar da wani taro da hukumomin kafafen yada labarai na jihar, wanda ya gudana a ma’aikatar yaɗa labarai da al’amuran cikin gida, karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar Ibrahim Abdullahi Waiya.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da daraktan ayyuka na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai Abba Sani Yola, ya fitar, sannan sanarwar tace hakan yazo don kawar yaɗa abubuwan da zasu kawo rashin zaman lafiya tsakanin al’ummar jihar.

Har ila yau, gwamnatin tace ɗaukar matakin baya daga cikin yunkurin dakushe muryar ƴan adawa, sai dai anyi hakan don samar da zaman lafiya.

Sannan an umarci masu gabatar da shirye shiryen siyasa dasu kiyaye yin tambayoyin da zasu sanya mutum bayar da amsa da ka’iya kawo tashin hankali. Daga bangaren mutanen dake yin magana a kafafen yaɗa labarai kuwa sanarwar tace dole sai in aka zo yin hira mutum ya saka hannu kan yarjejeniyar bazai ci zarafin kowa ba, ko kawo hargitsi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here