Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya roƙi ƴan kasuwa da masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje su shigo Najeriya domin samun damarmakin yin kasuwanci mai riba.
Sarkin ya nemi hakan yayin da yake jawabi a taron harkokin kuɗi, kasuwanci da zuba hannun jari na kasa da kasa, dake gudana a ƙasar Tunisia.
Yace a halin da ake ciki a Najeriya akwai damarmakin kasuwanci da cigaban tattalin arziki, wanda hakan zai bawa yan kasuwa damar samun riba a hannun jarin da zasu zuba.
Sarki Muhammad Sunusi, ya bayar da misali da Alhaji Aliko Ɗangote, wanda yake yin kasuwanci a Najeriya kuma yayi amfani da damarmakin kasuwancin kasar, har zuwa wannan lokaci da ya zama attajirin Afrika.
Har ila yau, ya nemi ƴan kasuwar su saka hannun jari a fannin noma, sarrafa kayayyaki da kimiyya da fasaha da sauran su.
Wata sanarwar da Galadiman Kano, Alhaji Munir Sanusi Bayero, ya fitar tace taron ya samu halartar fitattun mutane da suka haɗar da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ministar harakokin mata Hajiya Imaan Suleiman, da Ambasada Bolaji, wanda ya wakilci ƙaramar ministar harkokin waje Bianca Ojukwu.