Mayaƙan Boko Haram sun fara amfani da jirgi mara matuƙi—Yan majalisa

0
35
Sojin sama

Jaridar The Guardian, ta rawaito cewa Mambobin majalisun dokokin ƙasa, sun sanar da cewa mayaƙan Boko Haram na yin amfani da jiragen yaƙi mara matuƙi don kaddamar da hare hare kan yan Najeriya.

Daya daga cikin yan majalisar daya fito daga kudancin Borno, yace mayaƙan Boko Haram, suna amfani da makaman da suka fi karfinsu na sojojin kasar nan, wajen kai hare haren ta’addanci.

Dan Majalisar mai wakiltar Chibok, Ahmad Jaha, ya tabbatar da cewa da idon sa ya ga yadda Boko Haram, ke amfani da jiragen yaki mara matuƙi, irin wanda ko sojojin Najeriya basu da shi.

Zainab Gimba, wakiliyar mazaɓar Bama, a majalisar wakilai ita ma ta tabbatar da cewa mayaƙan na amfani da jiragen yaki marasa matuka, tana mai zargin akwai hannun ƙasashen waje a yadda Boko Haram ke samun malamai.

Yar majalisar tace an sanar da ita cewa akwai fararen fata a cikin mayaƙan Boko Haram, da haka ya ƙara tabbatar da cewa akwai sa hannun wasu ƙasashen waje a rashin tsaron da Boko Haram ta haddasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here