Ƴar takarar shugabancin kasar Amurka a zaɓen ƙasar na shekarar 2024, Kamala Harris, ta zargi shugaban ƙasar mai ci, wato Donald Trump, akan taɓarɓarewar sha’anin tattalin arzikin ƙasar tun bayan da ya hau mulkin Amurka.
Cikin kalaman nata yar takarar tace mulkin Trump, ya jefa Amurkawa cikin rashin tabbas, musamman akan manufofin sa.
Ko a yan kwanakin nan sai da wani rahoto ya nuna cewa Attajiran duniya sun yi asarar dukiyar da takai ta dala biliyan 300, a cikin kwanaki 100 na farko a mulkin Trump.
Ta ce abin da suka kasa ganewa shi ne, tsoratarwa ba ita ce kaɗai hanyar magance matsala ba, ƙwarin gwiwa ake buƙata.
Tattalin arziƙin Amurka ya samu koma baya a rubu’in farko na wannan shekarar, idan aka kwatanta da bunƙasar shi a shekaru hudu na mulkin tsohon shugaban kasar Amurka shugaba Joe Biden.