Man City ta lallasa Man United da ci 6-3 a Premier

0
129

Manchester City ta doke Manchester United da ci 6-3 a wasan makon na takwas a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Etihad.

Tun kan hutu City ta ci kwallo 4-0 ta hannun Phil Foden da Erling Haaland kowanne ya ci bibiyu.

Bayan da suka huta suka koma karawar zagaye na biyu Foden da Haaland kowanne ya kara zura kwallo a raga.

Sai dai United ta zare uku ta hannun Dos Santos, sannan Anthony Martial ya zura biyu a raga daya daga ciki a bugun fenariti.

Da wannan sakamakon City tana mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 20, United kuwa tana nan da makinta 12 tana ta shida a teburin wasannin bana.