Isra’ila na fuskantar gobarar daji mafi muni da ke ci gaba da tashi a wajen birnin Kudus.
Gobarar dai ta tilastawa mahukuntan Isra’ila kwashe dubban mazauna kasar cikin sa’o’i 24 kacal a daidai lokacin da kasar ta nemi taimakon kasashen duniya don taimakawa wajen yakar gobarar.
Sai dai kawo yanzu babu wani rahoto da ya nuna an samu asarar rayuka sanadiyyar tashin gobarar.