Barikin sojoji ta Giwa dake jihar Borno ta kama da wuta a cikin daren Laraba.
Wasu majiyoyi sun ce wutar ta tashi sakamakon kamawar gobara a rumbum adana makamai dake barikin, wanda hakan yasa bindigu da Bama bamai fashewa.
Sai dai majiyar Zagazola Makama, É—an jarida mai Sharhi akan harkokin tsaro tace an shawo kan lamarin da misalin karfe 1:30, na dare.
Majiyar tace ba harin yan ta’adda ne yayi sanadiyar tashin gobarar ba kamar yadda wasu suke yadawa. Amman sanarwar tace tsananin yanayin zafin da ake fama dashi ne yayi sanadiyar tashin gobarar da fashewar abubuwa.
Babu mutum ko É—aya wanda mutu sakamakon tashin wutar, sannan hankulan al’umma sun kwanta bayan komai ya daidaita.