Gwamnatin tarayya tace zata kawo karshen hatsarin motocin dakon fetur a fadin Nigeria

0
58

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamiti na musamman wanda zai riƙa yin aikin gano musabbabin yin hatsarin manyan motoci da motocin dakon fetur da kuma bayyana hanyoyin magance matsalolin yawaitar hatsarin.

Ministan sufuri Sanata Sa’id Alkali, ne ya bayyana a ranar Litinin data gabata lokacin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani da ma’aikatar sa ta shirya a birnin tarayya Abuja.

An shirya taron da manufar kaiwa ga wani mataki na tsare lafiya da dukiyar al’umma a faɗin Najeriya.

Babban aikin kwamitin shine bibiya da shirya shawarwarin yadda za’a magance yawaitar hatsarin manyan motoci da motocin dakon fetur.

Alkali, yace dole a fito da shirye-shirye na zahiri wanda zasu taimaka wajen magance afkuwar haduran.

Sanin kowa ne hatsarin manyan motoci da motocin dakon fetur na ɗaya daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama dasu, wanda hakan ke haddasa asarar rayuka da duniyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here