Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyar PDP a zaɓen shekarar 2023, kuma tsohon gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, yace kamata yayi a kyale shugaba Tinubu yayi shekara 8 akan karagar mulki in dai har cigaban Najeriya ake nema, da kuma saita ƙasa.
Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne Okowa, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ya bayyana hakan ne a yau Talata lokacin da ake tattaunawa dashi a gidan Talabijin na Arise.
Okowa, ya kasance wanda ya yiwa Atiku Abubakar, takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2023, yace saboda zaman lafiya da cigaban ƙasa an zabi Tinubu ya zama shugaban ƙasa, don haka a bari yayi shekara 8 sannan mulkin Najeriya zai iya komawa arewa.