Ƴan sanda sun kama angon da yayi sanadiyar mutuwar amaryar sa

0
21

Rundunar ƴan sandan Jigawa ta kama wani ango da abokan sa su uku, bisa zargin su da hannu a mutuwar amaryar sa a daren Asabar data gabata.

Da farko an zargi mijin ɗan kimanin shekaru 20, mai suna Auwal Abdulwahab, da haɗa kai da abokan sa, wajen tilastawa matar tasa ta amince yayi amfani da ita, amma taƙi yarda.

Rahotanni sun bayyana cewa ana tsaka da haka ne abokan suka yi amfani da karfi akan ta har hakan yayi sanadiyar mutuwar ta.

Sauran abokan angon sun haɗar da Nura Basiru, Muttaka Lawan, da Hamisu Musa, wanda suke a ƙauyen Tungo, na karamar hukumar Sule Tankarkar.

Bayan samun rahoton, jami’an yan sanda sun garzaya zuwa wurin, inda suka ɗauki gawar matar zuwa Asibitin ƙwararru na Gumel, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta, wanda tuni aka mika gawarta ga iyalanta domin yi mata jana’iza.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa, waɗanda ake zargin na fuskantar tuhumar kisan kai.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya umarci a tura lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na Jihar (SCID) dake birnin Dutse domin gudanar da cikakken bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here