Saudiyya ta haramtawa mazan ƙasar auren mata wasu ƙasashe

0
47

Saudiyya ta haramtawa mazan ƙasar auren mata daga Pakistan, Bangladesh, Chadi da Burma.

Jaridar Gulf News, ta rawaito cewa ƴan kasar Saudiyya da ke son auren mata daga kasashen waje sai sun fara samun amincewa daga hukumomin gwamnati wanda abin ya shafa sannan su mika takardar neman auren da suke son yi ta hannun hukuma.

Shugaban jami’an ƴan sandan Makkah Manjo Janar Assaf Qureshi, ya ce dole sai duk wata bukata ta aure daga wajen masarautar ta bi ta hanyoyi da wasu sharudda kafin a bayar da izini ko kin amincewa kafin yin aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here