Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa a fannin siyasa, Hakeem Baba Ahmed, yace ba saɓani ko rikici ne ya sanya shi ajiye muƙamin da shugaban ƙasa Tinubu ya bashi ba, sai dai ya ce babu alamar za’a yi abun da yake zato a tafiyar gwamnatin, kuma wannan ne dalilin sa na ajiye muƙamin.
Na shiga gwamnatin Tinubu da niyya mai kyau don na taimaka masa wajen gyara illar da Buhari ya yiwa arewa da Najeriya, sai naga hakan ba zai samu ba, daga nan na nemi waɗanda suka bani muƙamin mai taimakawa shugaban ƙasa a fannin siyasa su cire ni daga muƙamin, saboda naga babu alamun gyara a tafiyar, tunda da kyakkyawar manufa na karɓi aikin, inji Hakeem Baba Ahmed
Dattijon na arewa ya ƙara da cewa tunda ya fahimci inda Gwamnatin Tinubu, ta nufa ace ba da shi za’a yi wannan tafiya ba, saboda ba’a karɓar gyara ko yin abinda ya dace.
Tsohon mai taimakawa Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da BBC Hausa, yana mai cewa ya shiga gwamnatin Tinubu da niyyar tayi nasarar gyara barnar baya, ƙirƙiro sabbin hanyoyin haɗa kan ƙasa, samarwa matasa aikin yi, tsaro da sauran su, sai yaga burin sa bazai cika ba, wanda haka yasa ya ajiye muƙamin na don kar ya zama ɗaya daga cikin masu taimakawa wajen aikata ba daidai ba.