Gwamnatin tarayya zata cigaba da ciyar da daliban firamare

0
56

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta sake kaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.

Ƙaramin Ministan ma’aikatar jin ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu, ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.

Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara biyu akan mulki.

Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin Najeriya.

Yace shirin zai amfanar da ƙananun yara miliyan 10, inda yace ana kyautata zaton shirin zai sanya a samu ƙarin yaran da zasu shiga makarantun Boko da kaso 20 cikin ɗari, tare da karawa dalibai kokari.

Sake ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsananciyar yunwa, wanda hakan ke nuni da muhimmancin ɓullo da shirye-shirye makamantan wannan cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here