Gwamnan Kaduna ya kwace filaye da gidajen da Malam Nasir El-Rufa’i ya siyar 

0
140

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayar da umarnin ƙwace gidaje da filayen da tsohuwar gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta sayar.

Gidajen da filayen da aka ƙwacen sun haɗa da waɗanda tsohon gwamnan ya sayar a kwalejin Queen Amina da ke Kaduna da kwalejin Alhuda-huda da kwalejin Government Commercial da ke Zaria.

Umarnin kwace guraren na cikin wata sanarwar da aka fitar, a daren Talata mai ɗauke da sanya hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr AbdulKadir Mu’azu Meyere.

Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwace gidajen da filayen saboda amfanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here