Gwamnatin tarayya ta kare kanta daga masu sukar shirin sanya wuta mai amfani da hasken rana a fadar shugaban ƙasa.
Gwamnatin tarayyar tace fadar shugaban Amurka ma da Solar take amfani, inji Fadar shugaban Najeriya
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga, yace ba abun laifi bane idan fadar shugaban Najeriya ta saka wutar Solar, saboda ko fadar shugaban Amurka da ita take amfani.
Onanuga, ya bayyana hakan a matsayin martani ga masu sukar shirin gwamnatin tarayya data ware Naira biliyan 10, don sanya wuta mai amfani da hasken rana a Aso Rock.
Gwamnatin tarayyar dai tace tsadar kuɗin wutar lantarki ne yasa ake shirin sanyawa fadar shugaban kasar wuta mai amfani da hasken rana.