Rundunar Hisbah ta rushe gurin da ake cewa Sawun Annabi Muhammad (SAW) ya fito

0
46

Rundunar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani taɓo da aka ce an ga sawun Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a cikin sa a jihar Kano.

Jaridar Leadership ta rawaito cewa wajen, a unguwar dakata, an share shi domin yin aikin titin jirgin ƙasa da zai bi ta wajen, amma sai mutane su ka maida shi wani waje mai tsarki na ibada saboda an ga ruwa ya na fitowa a wajen.

An ga wani faifen bidiyo da ya karade kafofin sadarwa inda mutane ke tururuwar zuwa wajen domin yin kallo, wasu kuma na ɗiban ruwan da nufin cewa ruwa ne mai tsarki da za su samu albarka da samun lafiya tunda wai sawun Annabi ne a wajen.

Sai dai kuma tuni hukumar ta Hisbah, ta bakin Mataimakin Kwamandan hukumar, Malam Mujahideen Aminuddeen ya ce an rushe wajen kuma an kori mutane.

A cewar sa, shirme ne da kuma jahilci, duba da cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama bai taba taka nahiyar Afrika ba.

Malam Mujahideen ya ce irin wannan ta’adar kan janyo Musulmi ya rasa imanin sa, inda yayi kira ga masu aikata hakan su yi gaggawar tuba su kuma daina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here