Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, yace ƴan siyasar yankin arewa sun gaza yiwa yankin abinda ya dace na cigaba, yana mai cewa dole ne su nemi afuwa daga wajen al’umma.
Uba Sani, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da talabijin ta Trust TV.
A tattaunawar gwamna Uba Sani, yace dole a kyale mutane su soki Gwamnati a inda tayi ba daidai ba don samun gyara.
A cewar sa duk ɗan siyasar arewa da ya kwashe shekaru 20 yana yin siyasa ya zama wajibi akan sa ya nemi yafiyar al’ummar yankin saboda cin amanar da suka yiwa arewa.
Dole na fadi gaskiya, dukkan mu, har ni, Nima nayi majalisar dattawa amma har yanzu matsalolin Arewa sun dade su na faruwa kuma har yanzu na gaza magance su, inji shi