Fadar shugaban ƙasa ta zargi gwamnonin jihohi da gaza yin abinda ya dace wajen tallafawa yunkurin da ake yi na kakkaɓe ta’addanci, musamman a jihohin da rashin tsaro ya ta’azzara.
Hakan yazo a daidai lokacin da rashin tsaro ya yawaita a jihohin Benue, Enugu da Plateau, sannan wannan na ƙara fargaba akan zaman lafiya a Najeriya baki ɗaya.
Mai taimakawa shugaban ƙasa a fannin tsare-tsare da sadarwa Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wata kafar talbijin, yana mai cewa gwamnoni basa yin amfani da kuɗaɗen da ake aike musu dashi na tunkarar ƙalubalan tsaro, da kuma ƙin tallafawa hukumomin tsaro a jihohin su.
Bwala, yace duk da maƙudan kudaden da ake ware wa fannin tsaro gwamnoni basa iya bawa ƴan sanda da sojoji da DSS, kuɗin da zai taimaka suyi ayyukan su.
Yace wasu gwamnonin basa ware wa fannin tsaro kuɗin daya wuce Naira miliyan 20 a kowanne wata, inda yace adadin yayi kaɗan, saboda gwamnatin tarayya tana basu kuɗin da yakai Naira biliyan 3 don sha’anin tsaro kawai.
Daniel Bwala, ya ƙara da cewa tabbas rashin isasshen kuɗi ga hukumomin tsaro na taimakawa wajen lalata harkokin samar da zaman lafiya.