Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gadar da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a ƙaramar hukumar Gujiba da ke jihar Yobe.
Tarwatsa gadar yazo mako ɗaya bayan da ‘yan ta’addan suka lalata gadar Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno.
Wata majiya ta shaidawa Zagazola Makama, cewa harin ya afku da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar.
Harin ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran su, saboda gadar na kan hanyar Katarko zuwa garin Goneri.