Sojoji sun kubutar da wata ‘yar makarantar Chibok da tagwayen jarirai

0
102

Dakarun Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas, sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram da ba a tantance adadinsu ba, tare da kubutar da wata ‘yar makarantar Chibok, wadda ta haifi tagwaye a lokacin da aka yi garkuwa da su.

Sojojin tare da hadin guiwar CJTF sun cimma wannan nasara ne a ranar 29 ga Satumba, 2022 bayan da suka kai farmaki a yankin Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād.

Wani rahoton sirri da aka samu daga manyan majiyoyin soji na Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, kuma ya samu ga wakilinmu, ya nuna cewa sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addar, inda suka yi nasarar kawar da dama daga cikinsu a cikin lamarin, yayin da kuma aka yi nasarar dakile su. wasu da dama sun tsere da munanan raunukan harbin bindiga.

“A yayin arangamar, sojoji sun yi nasarar ceto Yana Pogu, ‘yar Chibok, wacce ke lamba 19 a jerin ‘yan matan da suka bata tare da ‘ya’yanta hudu.

“An same ta da wasu tagwaye ‘yan watanni hudu a cikin wani yanayi mara kyau.

“Wasu daga cikin ‘yan ta’addar da suka tsere sun yi yunkurin yi wa sojoji kwanton bauna amma yayin da suke aiki da bayanan sirri, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa da karfin wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa.

“An ceto karin mata bayan haduwarsu. An mayar da su runduna ta 21 Bama, domin kula da lafiyarsu,” inji majiyar.

Wakilinmu ya tuna cewa a watan Afrilun 2014 ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa da dalibai mata 276 yawancinsu Kiristoci ‘yan tsakanin shekaru 16 zuwa 18 a makarantar Sakandaren ‘yan mata ta gwamnati da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

Ya zuwa yanzu kusan 100 daga cikin ‘yan matan na nan a yankunan ‘yan ta’addar, yayin da wadanda suka yi sa’a ko dai sojoji ne suka kubutar da su ko kuma sun kubuta daga hannun ‘yan ta’addan.