Isra’ila na neman kaiwa tashoshin nukiliyar Iran hari

0
41

Yan siyasar Isra’ila sun yi kira da a kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

An samu wannan bayani bayan fitar wani rahoto da ba a tabbatar ba, wanda ke cewa Amurka ta yi watsi da shirin kai harin.

Tsohon ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz, ya bayyana shugabannin Iran a matsayin ƙwararru a dabarun jan ƙafa kuma ya ce dole ne Isra’ila ta kai hari kan Iran.

BBC tace da take ambato majiyoyin hukuma da ba a bayyana sunayensu ba, jaridar New York Times ta ce Isra’ila na son Amurka ta taimaka wajen aiwatar da wannan shirin kai harin a watan Mayu mai zuwa.

Amma a makon da ya gabata, shugaba Trump ya bayyana cewa Amurka na tunanin tattaunawa da Iran.

Za dai a ci gaba da tattaunawa kan lamarin a birnin Rome a ranar asabar mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here