An kama ɗaruruwan mayaƙan Boko Haram a Lagos

0
43

Kwamandan rundunar ƴan sa kai ta jihar Lagos Kumar Sanda, yace sun kama ɗaruruwan mutane da ake zaton mayaƙan Boko Haram, ne dake shigowa jihar daga arewa.

Sanda, ya bayyana hakan a lokacin da wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta karrama rundunar ƴan sa kan, da lambar yabo akan cewa sun fi kowacce kungiyar tsaro yin abun da ya dace a Lagos.

Yace suna mayar da hankali wajen sanya idanu a ɗaukacin guraren da ke tara al’umma irin su tashar motoci, kasuwanni, sa sauransu inda a nan ne yan arewa ke sauka don yin ci rani, sannan yace a irin wannan aiki da suke yi an kama dubban yan Boko Haram.

Kumar, ya ƙara da cewa babban burin su shine hana yan ta’addan arewa shigowa Lagos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here