Tafiyar Tinubu Faransa tasa an kashe ƴan Najeriya 150—Peter Obi

0
27

Ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya buƙaci Shugaban ƙasa Tinubu da ya dawo gida Najeriya ba tare da ɓata lokaci ba domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara.

Obi ya bayyana hakan a shafinsa na X, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a jihohin Filato, Zamfara, Borno da sauran su.

Idan za’a iya tunawa dai shugaba Tinubu ya tafi ƙasar Faransa a ranar 2 ga Afrilu wanda akace zai shafe makonni biyu a wata ziyarar aiki.

 Daniel Bwala, Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Manufofi, ya ce tafiyar nada muhimmanci wajen yin bitar tsare-tsaren gwamnatin tarayya da kuma sauye-sauye, gabanin cikar Tinubu shekaru biyu na akan mulki.

A cikin saƙon daya fitar a ranar Laraba, Obi ya ce ya zama dole ya ja hankalin shugaban ƙasa don ya fuskanci ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke ciki.

Ya bayyana cewa, wannan kira nasa na gaggawa ya zama dole saboda ƙaruwar ta’addanci da miyagun laifuka a faɗin Najeriya, tare da rashin ganin matakan da gwamnati ke ɗauka a zahiri.

Yace akalla mutane 150 aka kashe cikin makonni biyu da Tinubu ya shafe a Faransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here