Majalisar wakilai ta gayyaci gwamnan riƙon jihar Rivers

0
58

Kwamitin majalisar wakilai mai sanya idanu akan al’amuran riƙon ƙwarya a Rivers ya gayyaci gwamna Ibok Ete Ibas, don tattaunawa dashi akan wasu abubuwan da suka shafi jihar tun bayan da ya karɓi riƙon ƙwarya.

Mai magana da yawun majalisar Aikin Ritimi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar daya fitar a yau Laraba, yana mai cewa Ibok zai gurfana a ranar Alhamis mai zuwa.

Shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, ne ya ƙaddamar da kwamitin a ranar talata data gabata, wanda ya ƙunshi mutane 21.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here