Shugaban ƙasa Tinubu ya bayar da umurnin kawo karshen duk wani rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar 2025.
Shugaban ya bayar da umurnin ga ɗaukacin hukumomin da suke da alhakin tabbatar da tsaron ƙasa.
Ministan tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ne ya shaidawa BBC hakan, inda ya ce hukumomin tsaro sun dukufa sosai domin tabbatar da hakan.
A cewar Badaru, Tinubu ya bada umarni kan cewa duk abin da ake ciki na matsalar tsaro a Najeriya baki ɗaya ta ƙare zuwa ƙarshen wannan shekarar.
A baya bayan nan dai rashin tsaro na ƙara ta’azzara a jihohin arewa musamman Zamfara, Borno, Filato da sauran su.