Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama matashin dake yin ma’amala da Akuya saboda yayi suna (trending) a kafafen sada zumunta.
Matashin mai suna Shamsu Yakubu, ya kasance dan shekara 24, ɗan asalin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano.
Shamsu, shine ya bayar da damar a É—auke shi a hoto mai motsi lokacin da yake yin ma’amala da Akuyar, don ya samu mabiya a shafukan sada zumunta biyo bayan yadda matasa ke yin rige-rigen Æ™irÆ™iro wasu abubuwan da zasu sanya su yin suna.
Bidiyon da aka yaÉ—a ya bayyana yadda Shamsu Yakubu, ke sanya bakin sa yana tsotsar tsiraicin wata Akuyar da ya rike ta da hannun sa.
Ganin haka ne yasa al’ummar garin da matashin ke yin rayuwa suka yi kokarin É—aukar matakin ladabtawa akan sa, sai dai kafin hakan dagacin garin ya kaiwa hukumar Hisbah korafi don kar a karya doka wajen yiwa Shamsu hukunci.
Mukaddashin babban kwamandan rundunar Hisbah ta jihar Kano Dr. Mujahiddin Aminudden, ya bayyana cewa Shamsu Yakubu, yana hannun su, kuma za’a yi masa gwajin Æ™waÆ™walwa dana ta’ammali da miyagun kwayoyi don tabbatar da lafiyar sa, kafin hukunta shi.