Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya bayar da kyautar gida da ɗaukar nauyin karatun yaron nan da malamin sa yaci zarafin sa ta hanyar yi masa dukan da ya wuce misali.
Hakan ya biyo bayan kama malamin da ake zargi da aikata lefin dukan dalibin a ranar Asabar data gabata a birnin Maiduguri.
Zulum ya bayyana damuwarsa akan lamarin yana mai cewa hakan ba abun kyalewa bane, sannan yace dole ne a kula da lafiyar ƙananun yara da basu hakkin su ba tare da cutar da su ba.
Dalibin mai suna Bashir, ya kasance Maraya sakamakon rasuwar da mahaifiyar yayi sanadiyar rikicin Boko Haram.