Ƴan bindiga sun kashe jami’in Civil Defence 

0
90

Ƴan bindiga sun kashe jami’in rundunar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, bayan yiwa tawagar jami’an tsaron kwantan ɓauna lokacin da suke yin atisaye a yankin Igbomotoru dake karamar hukumar Ijaw ta kudu a jihar Bayelsa.

Kawo yanzu ba’a bayyana sunan jami’in da aka kashe ba, wanda abun ya faru a ranar juma’a.

Daily trust, ta rawaito cewa jami’an na Civil Defence, sun gamu da harin a lokacin da suke kan hanyar dawo wa daga wajen dakile satar danyen man fetur.

Wata majiya tace yan bindigar da suka kai harin sune suka taɓa bude wuta akan jirgin ruwan jami’an Civil Defence masu yaki da satar danyen man fetur a yankin Koluama.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar Civil Defence a jihar Bayelsa Solomon Ogbere, domin jin ta bakin sa akan faruwar lamarin cewa yayi bai kai ga kammala tattara bayanai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here