Gwamnatin Tarayya zata kula da lafiyar ‘Yan Nijeriya milyan 83 kyauta

0
113

Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf dangane da al’amarin kula da lafiyar ‘yan Nijeriya milyan 83 kyauta da ke cikin wadanda ya kamata a taimakawa.

Janar Manaja na hukumar kula da inshorar lafiya ta kasa shiyyar Ilorin Mista Adelaja Abereoran, shi ne wanda ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da Jaridar LEADERSHIP a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.

Abereoro yana kulawa ne da Jihohin Kwara, Kogi, da kuma Neja.

Ya ce gwamnatin tarayyar ta dauki matakin ne domin lurar data yi yawancin mutane ba su iya daukar nauyin kulawa da lafiyarsu, kamar yadda ya kamata.

Ya ci gaba da bayanin cewa akwai wani tsarin na wata dokar da aka yi ma kwaskwarima “ da ta bada dama ta kafa hukumar kula da inshorar lafiya bautar kasa, domin a samu damar kulawa da ‘yan Nijeriya milyan 83,wadanda suke da bukatar haka amma ba za su iya ba kamar yadda Abareoro ya bayyana”.

Ya yi kira da gwamnatocin Jihohi da su taimakawa kokarin da gwamnatin tarayya take yi na wajen kafa ita hukumomin inshorar lafiya, domin tallafawa mutane da yawa samun damar yadda za a kula da lafiyarsu kamar yadda ya dace a Jihohi.

Ya kara jaddada cewa Nijeriya ba zata iya cimma hakan ba,ba tare da taimakon Jihohi ba da sauarn masu ruwa da tsaki a bangaren daya shafi lafiya.

Abereoro ya yi kira da ‘yan majalisun tarayya su sa tsarin samar da inshorar lafiya a cikin ayyukan mazabunsu, domin kamar yadda ya ce hakan zai taimaka matuka.

Bugu da kari an kara inganta ayyukan hukumar don su tafai kafada-kafada da kamar yadda ake yi a kasashen duniya,yanzu kuma a karkashin tsarin za a dub duk irin matsalar kula da lafiyar da mutane suke fama da ita.

Daga karshe duk dai a karkashin sabon tsarin dokar, masu yi ma kasa hidima suma suna daga cikin wadanda za su amfani da inshorar kula da lafiya,duk daga ranar da suka iso wurin da aka tura su.

Wannan kuma har zuwa ranar da za su kammala aikin bautar kasa,wannan ya hada da mata da suke cikin aikin yi ma kasa hidima wadanda suka samu Juna Biyu cikin shekarar da suke yin aikin yi kasa hidima.