An fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasar Gabon

0
40

Al’ummar ƙasar Gabon sun soma kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasar wanda ke gudana a yau Asabar.

Zaɓen shine karon farko tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin ƙasar watanni 19 da suka wuce domin kawo ƙarshen mulkin iyalan Bongo waɗanda suka shafe fiye da shekaru hamsin a kan karagar mulki ba tare da bawa wani damar mulkin ƙasar ba.

Zaɓen shine ke tabbatar da cewa an kawo karshen mulkin da sojoji ke yiwa Gabon bayan yin juyin mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here