Sanatan Borno ya nemi ministan labarai ya dena siyasantar da harkokin tsaro

0
117

Sanatan dake wakiltar Borno ta tsakiya Kaka Shehu Lawan, ya nemi ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Muhammad Idris, da ya mayar da hankali akan aikin sa, sannan ya dena siyasantar da harkokin rashin tsaro.

A ranar Talata ne gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, lokacin gabatar da wani taron majalisar tsaron jihar, ya janyo hankalin gwamnatin tarayya akan cewa yan ta’addan Boko Haram na ƙoƙarin mamaye Borno baki ɗaya.

Ya bayyana cewa janye sojoji dake wasu yankunan da suke bayar da tsaro na daga cikin dalilan farfaɗowar ayyukan rashin tsaro a Borno.

Sai dai ministan yaɗa labaran a ranar Laraba ya fitar da wata sanarwar daya ƙalubalanci gwamna Zulum akan cewa gwamnatin tarayya har yanzu tana kan kokarin dakile ayyukan ta’addanci a sassan Najeriya.

Ya kuma ce jami’an tsaro suna yin aiki babu dare babu rana wajen kakkaɓe ta’addanci a jihar Borno.

Shima a nasa jawabin Sanata Kaka Shehu Lawan, a yau Alhamis ya bayyanawa manema labarai cewa akwai bukatar ministan yaɗa labaran ya rika yin koyi da magabatan sa, da suka gudanar da kyakkyawan aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here