An shiga firgici lokacin da aka tsamo gawarwakin mutane uku a cikin kogi duk an cire kawunan su

0
63

An shiga firgici lokacin da aka tsamo gawarwakin mutane uku a cikin kogi duk an cire kawunan su a jihar Ondo.

An samu gawarwakin mutanen a kogin dake tsakanin garuruwan Ore da Odigbo, sai dai mutanen da aka samu an kashe É—in ba Æ´an asalin jihar Ondo bane.

Lamarin daya faru a ranar Lahadi data gabata ya tayar da hankalin al’ummar dake yankin, duk da cewa wani da aka ciro gawarwakin a gaban idon sa yace ana kyautata zaton cewa an kashe mutanen domin ayi tsafi da sassan jikin su, kafin a jefar da gawar su a Kogi.

Al’ummar gari ne suka sanar da jami’an tsaro lamarin bayan ganin gawarwakin.

Kakakin rundunar Æ´an sandan Ondo Olayinka Alayande, ya tabbatar da kisan mutanen inda yace za’a gudanar da cikakken binciken da zai sanya a gano asalin waÉ—anda aka kashe É—in, da kuma sanadiyar mutuwar tasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here