Gwamnan riƙon jihar Rivers ya saɓawa umarnin kotu

0
53

Gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya, ya amince da nada shugabannin riko na ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Prof. Ibibia Lucky Worika, ya fitar a ranar Laraba a Port Harcourt, ta ce Ibas ya kuma amince da sake kafa wasu Hukumomi, Kwamitoci, da ma’aikatu da aka dakatar da su a baya.  

Sanarwar ta kara da cewa, duk wadannan nade-naden sun fara aiki daga ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025.  

Sai dai kuma hakan na zuwa kasa da sa’o’i 24 bayan da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta hana shi nada shugabannin da za su rika kula da al’amuran kananan hukumomin.

Mai shari’a Adam Muhammed ne ya bayar da a wannan umarni a ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here