Likitoci dubu 16 sun fice daga Najeriya—Gwamnatin tarayya

0
29

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa likitoci dubu 16 sun bar Najeriya a cikin shekaru 5.

Ministan lafiya Muhammad Pate, ne ya sanar da hakan yayin wani taron ƙara wa juna sani na ƙungiyar likitoci ta (AMCOA) daya gudana a ranar Talata, inda yace hakan ya jawo wa Najeriya asarar biliyoyin kuɗi.

Ya ce ƙiyasin kuɗin da ake kashewa wajen bai wa likita ɗaya horo a Najeriya ya zarta dala 21,000, inda ya nuna damuwa game da yadda kasar nan ke asarar irin kuɗaɗe masu yawa wajen horas da likitocin.

Minista Pate, ya kara da cewa hakan yana shafar ɓangaren kula da lafiya sosai, inda yankunan ƙauyuka suka fi shiga haɗarin rashin likitoci.

Yace a yanzu yawan mutanen da likita ɗaya ke gani a Najeriya ya ƙaru zuwa miliyan 3.9, wanda ya zarta adadin da hukumar lafiya ta duniya ta ƙiyasta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here