Gwamna Babagana Umara Zulum, na jihar Borno ya bayyana cewa sake farfadowar hare-haren Boko Haram da sace-sacen mutane a kusan kullum a wasu al’ummomi ba tare da wani martani ba yana nuna cewa jihar Borno ta rasa iko a yakin da ake da Boko Haram ba.
Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taro na Musamman akan tsaro wanda ya samu halartar Kwamandan Rundunar Sojoji ta 7, Manjo Janar Abubakar Haruna, da Kwamandojin Sassa, Kwamishinan ‘Yan Sanda, da shugabannin sauran hukumomin tsaro, Shehun Borno, Alhaji Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi, Shehun Bama, Sarakunan Biu, Uba, Askira, da Gwoza.
Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bayar da cikakken goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro a yakin da ake yi da Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda, wanda hakan ya samar da d zaman lafiya cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai ya nuna damuwa kan sabbin hare-hare da korar dakarun soja daga wuraren da suka hada da Wajirko, Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a karamar hukumar Gwoza, da kuma kisan gilla da ake yi wa fararen hula da jami’an tsaro, yana mai cewa lamarin yana bukatar kulawa ta musamman kuma yana mayar da Borno da yankin Arewa maso Gabas baya.