Sanata Ali Ndume ya sake caccakar Shugaban ƙasa Tinubu

0
55

Sanatan kudancin Borno Ali Ndume, ya ƙalubalanci Shugaban ƙasa Tinubu akan yadda yake yin naɗe naɗen mukamai, wanda yace ana saɓawa ka’idojin aikin gwamnatin tarayya.

Ndume, yace naɗe naɗen Tinubu ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa sashi na 14(3) akan sanya kowane ɓangare a mukaman gwamnatin tarayya da yin adalci ga kowa.

A lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta Arise, a ranar Litinin Ndume ya zargi shugaban ƙasa Tinubu da gaza yin adalci a tsakanin kabilu da yankunan Najeriya wajen raba mukamai.

Ali Ndume, dai yayi kaurin suna wajen ƙalubalantar wasu daga cikin manufofin jam’iyyar APC da kuma gwamnatin tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here