Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, yayi liyafar cin abinci da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers da aka dakatar.
Mai taimakawa Wike a fannin sadarwa da kafafen sada zumunta Lere Olayinka, ya bayyana cewa ministan ya samu damar yin liyafar a ƙasar Birtaniya, a ranar Litinin.
Lere Olayinka, yace Wike ya bar Najeriya zuwa Birtaniya a cikin daren Lahadi domin samun damar ganawa da ƴan majalisar.
Kafin tafiyar tasa zuwa Birtaniya Wike ya samu damar ganawa da abokan siyasar sa dake jihar Rivers.
Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers da aka dakatar Martin Amaewhule, yace sun je ƙasar Birtaniya domin sake samun ƙwarewa a aikin majalisa.