Tsawa ta kashe shanu masu yin kiwo a jihar Ondo

0
44

Faɗowar tsawa ta kashe shanu takwas a jihar Ondo.

Lamarin ya faru a garin Ori-Ohin na ƙaramar hukumar Ose, a yammacin ranar Lahadi lokacin da ake yin ruwan sama mai ƙarfi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Olayinka Ayanlade, ya bayyana wa kafar talabijin ta Channels cewa shanun sun gamu da tsautsayi ne amma ba wani ne ya kashe su ba.

Ya ƙara da cewa tuni rundunar ta fara ɗaukar mataki saboda kar lamarin ya haifar da fitina.

Channels ta ce irin wannan lamari ya taɓa kashe shanu 36 a shekarar 2019 lokacin da tsawa ta faɗawa yankin Ifedore na jihar ta Ondo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here