Al’ummar ƙaramar hukumar Funtua dake jihar Katsina sun bayyana cewa ƴan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan su, inda suka sace kananan yara da mata sama da 50.
Maharan sun kuma kashe akalla mutum 6, lokacin da suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume.
Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita bah ar zuwa ranar Lahadi da rana, kamar yadda BBC ta rawaito.
Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Garaa ne na ƙaramar hukumar Funtua, ya ce Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53.