Asirin likitan bogi ya tonu bayan ya kashe tsohon shugaban gunduma na APC a Bauchi

0
115

Jami’an tsaro a jihar Bauchi sun kama wani Andrew Godwin da ake zargi likitan bogi kan halaka wani majinyaci yayin tiyata.

Rahotanni daga garin Bogoro sun bayyana cewa Godwin ya shafe shekaru yana yi wa mutane da ba su ankare ba tiyata kuma daga bisani su mutu.

Bincike ya nuna cewa Andrew yana da kemis na sayar da magunguna amma ba shi da lasisi ko satifiket na yi wa mutane tiyata.