Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun ƙaramar Sallah

0
55

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranakun hutun Sallah ƙarama.

Gwamnatin tace Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu sune ranakun hutun.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar a yau ɗauke da sanya hannun babban sakataren ta Magdalene Ajani.

Sanarwar ta rawaito ministan harkokin cikin Olubunmi Tunji-Ojo, na riƙon musulmai suyi amfani da lokacin bukukuwan Sallah ƙarama don yiwa Najeriya addu’ar samun nasara da zaman lafiya, da kuma nunawa juna ƙauna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here