An rantsar da Janar Abdouramane Tchiani, a matsayin wanda zai shugabanci jamhuriyar Nijar tsawon shekaru 5 kafin miƙa mulki ga farar hula.
Rantsuwar wani bangare na aiwatar da shawarwarin da aka cimma yayin babban taron Nijar da ya gudana a watan Fabrairu.
A lokacin shan rantsuwar a ranar Laraba, Tchiani ya zama babban janar É—in soja mai taurari biyar.
Manyan masu ruwa da tsaki da jami’an soji ne suka halarci taron rantsuwar na yau daya gudana a babban É—akin taro na birnin Yamai.
An gudanar da taron a yau Laraba, wanda hakan ya bawa shugaban damar cigaba da riƙe jamhuriyar Nijar bayan kifar da Gwamnatin Bazoum.