Mikel ya sanar da yin murabus daga kwallon kafa

0
130

Fitaccen tauraron dan kwallon Najeriya, Mikel Obi ya sanar da cewa ya yi murabus daga kwallon kafa.

Tsohon dan wasan na kungiyar Chelsea ya bayyana hakan ne a ranar Talata a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Obi ya ce komai da ke da farko dama yana da karshe kuma ya gamsu da irin nasarori da darussan da ya koyi cikin shekaru 20 na buga kwallo.